Connect with us

Featured

Gwamnan Kano ya naɗa shugaban ƙungiyar ƴan jaridun yanar gizo a matsayin sabon MD na Radio Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin Hisham Habib shugaban kungiyar ƴan jaridu ta yanar gizo reshen jihar Kano a matsayin Manajan Daraktan gidan rediyon Kano.

Naɗin wanda ya fara aiki nan take a wata sanarwa da Hisham ɗin ya fitar, wanda kuma ke rike da muƙamin muƙaddashin mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hisham Habib gogaggen ɗan jarida ne, ya yi digirinsa na farko a fannin turanci a jami’ar Bayero Kano, sannan ya yi digiri na biyu a fannin koyon aikin jarida.

Kafin wannan naɗin, Hisham ya yi aiki a matsayin ma’aikaci a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano kuma ya riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a a ma’aikatar shari’a.

Har ila yau, ya yi aiki a matsayin mai ba da rahoto a fitattun kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da jaridar Daily Trust da Daily Independent.

Bugu da kari, ya yi aiki a matsayin shugaban Media Cave Limited, wata kafar yada labarai mai zaman kanta kuma mawallafi a jaridar News Tunnel.

Ana sa ran naɗin Hisham zai ƙara inganta ayyukan gidan rediyon Kano da kuma ƙara azama wajen isar da aiki mai inganci ga al’ummar jihar Kano da da maƙwambtan jihohi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet