Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawu rundunar na ƙasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Talatar makon nan.
Sanarwar ta ce, tura kwamishinonin ya biyo bayan shawara da hukumar ƴan sanda ta bayar, inda kuma babban sufetan ya amince da hakan.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, tura sababbin kwamishinonin zai taimaka wajen ƙara samar da tsaro mai inganci.
