Connect with us

Labarai

NEMA Ta Fadakar Da Wasu Jihohi Da Za Su Iya Fuskantar Ambaliya

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta lisafta wasu jihohi 14 da kananan hukumomi 31 da ka iya samun samun ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan shiyya na NEMA, a ofishin yankin Legas.

Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya jero jihohi da kananan hukumomi kamar haka:

 

A jihar Plateau: akwai kananan hukumomin Langtang, da Shendam

A jihar Kano kuwa: akwai kananan hukumomin Sumaila, da Tudun wada

Daga jihar Sokoto: akwai kananan hukumomin Shagari, Goronyo, Silame

Daga jihar Delta: akwai karanar hukumar Okwe

Jihar Kaduna: akwai karamar hukumar Kachia

A jihar Akwa Ibom: akwai karamar hukumar Upenekang

Jihar Adamawa: akwai kananan hukumomin Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta, Yola

A jihar Katsina: akwai kananan hukumomin Katsina, Jibia, Kaita, Bindawa

Sai jihar Kebbi: akwai kananan hukumokin Wara, Yelwa, Gwandu

Sai kuma jihar Zamfara: akwai kananan hukumomin Shinkafi, Gummi

A Jihar Borno: akwai karamar hukumar Briyel

Sai kuma jihar Jigawa: akwai karanar hukumar Gwaram

Daga jihar Kwara: akwai karamar hukumar Jebba

Jihar Niger kuwa: akwai kananan hukumomin Mashegu, da Kontagora

Farinloye ya godewa Hukumar da ke gargadi kan ambaliyar ruwa (FEWS) Central Hub na Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Abuja bisa raba bayanan. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet