Labarai
Gwamna Abba kabir Yusuf ya yi ganawar farko da kwamishinoninsa
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba kabir Yusuf, ya yi ganawar farko da kwamishnoninsa a yau Laraba.
Da yake gabatar da jawabinsa yayin ganawar tasu, Gwamnan ya taya su murna bisa zaɓarsu da aka yi a kan wannan matsayi.
Gwamnan ya kuma ce, an zaɓo su ne bisa irin jajircewar da suke da ita a wuraren da suka yi aiki a baya.
Haka kuma gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ja hankalin kwamishnonin da su kasance masu aiwatar da ayyukansu bisa gaskiya da amana.
Haka kuma, ya yi kira a garesu da da cewa lallai ne ya ga canji a ayyukan da za su tun kara nan da watanni shida a dukkan ma’aikatunsu, domin ta hakan zai tabbatar da kwazonsu.
