Labarai
Gwamnatin Kano Ta Janye Karar Dakatar Da Binciken Ganduje Kan Bidiyon Dala
Gwamnatin Jihar Kano ta janye karar da ta shigar gaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati ta Kasa EFCC inda take neman ta hana ta ci gaba da gayyato, bincike, ko yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje tambayoyi.
Sanarwar janye karar da aka gabatar a gaban babbar kotun tarayya ta Kano na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban mai shari’a na Kano kuma kwamishinan shari’a, Haruna Isa Dederi, mai kwanan wata 4 ga watan Yuli 2023, kuma aka aika wa Sanusi Musa, kamar yadda SAN ta ruwaito The PUNCH.
An rubuta cewa, “Mun rubuto ne domin sanar da ku cewa Gwamnatin jihar Kano da Babban Lauyan Jihar Kano na son su yi muku bayani kan umarnin da aka ba ku a baya, da aka ba ku don gudanar da shari’a mai lamba NO: FHC/KN/71/2023 tsakanin Babban Lauyan Jihar Kano da Hukumar yaki da Yiwa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC).
Maido da martabar Kano da aka bata, Gwamna Abba Yusuf ya fadawa sabbin kwamishinonin
“Don haka ann umurce ka da ‘yan tawagar ka da kada ku kara daukar wani mataki kan lamarin, ko dai ta hanyar gurfana a gaban kotu ko kuma shigar da duk wata kara da ta shafi shari’ar,” in ji Babban Lauyan Jihar Kano.
Ku tuna cewa gwamnatin jihar Kano a karkashin tsohon gwamnan ta hannun ma’aikatar shari’a ta fitar da wata takarda don hana EFCC gudanar da bincike kan bidiyon dala da ya janyo cece-kuce.
