Labarai
Sokoto: Gwamna Aliyu Ya Kullewa Ma’aikatan Gidan Gwamnati Kofa Saboda Makara
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto a ranar Alhamis ya kulle kofar gidan gwamnati ga ma’aikatan da suka zo a makare.
An ce gwamnan ya tuka kansa zuwa gidan gwamnati da misalin karfe 8:30 na safe sai dai ya gano cewa yawancin ma’aikatan ba sa ofisoshinsu daban-daban.
Ya hadu da masu aikin goge-goge da shara da ma’aikaciyar jinya daya a asibitin gidan gwamnati.
Sai dai ya umurci jami’an tsaro da su kulle kofar gidan kuma kada su bari kowa ya shiga.
An tattaro cewa kofar ta kasance a rufe har zuwa karfe daya na rana.
Jaridad Daily Trust ta gano cewa an kullewa manyan ma’aikata da dama ciki har da wasu daga cikin hadiman gwamnan.
Yayin da yake tabbatar da hukuncin nasa, Aliyu ya bayyana cewa, “Wannan ba abin wasa ba ne.
“Abin da ake tsammani daga kowace gwamnati mai mahimmanci shi ne tabbatar da biyan albashin ma’aikata a kan lokaci.
“Lokacin da na shigo, na biya albashin watanni biyu a cikin makonni uku.
“Shi ya sa na tuka kaina zuwa ofis saboda direbobi na ba su zo kan lokaci ba.
“Amma ba zan gaya muku mataki na na gaba ba saboda ku ma kun zo a makare (yana nufin ‘yan jarida),” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa “Na yi wa al’ummar jihar Sokoto alkawarin cewa ba zan ci amanarsu ba, kuma ba zan bar wani jami’in gwamnati ya yi hakan ba.
“Ku yi aiki ko ku mayar mana da kuɗinmu. Ba za ku iya karbar kudinmu ba tare da cancantar su ba,” inji shi.
