Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Na Jigawa Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoninsa

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 bayan majalisar dokokin jihar ta tabbatar da su.

An gudanar da bikin ne a dakin taro na gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.

Gwamnan ya baiwa sabbin kwamishinonin da aka nada wuraren da zasu yi aiki, sannan ya kuma yi kira a gare su da jajircewa wajen ganin an aiwatar da ajandar gwamnati mai dauke da abubuwa 12.

Sabbin kwamishinonin sun hada da Ibrahim Babangida Umar Ministry (Ma’aikatar Kasafi da Tsare Tattalin Arziki), Farfesa Hannatu Sabo Muhammad (Ma’aikatar Kudi), Dr Muhammad Abdullahi Kainuwa (Ma’aikatar Lafiya), Aminu Kanta (Ma’aikatar Kasuwanci), da Ahmed Garba MK (Ma’aikatar Kananan Hukumomi).

Sauran sun hada da Ibrahim Garba Hannun Giwa (Ma’aikatar Albarkatun Ruwa), Dr Lawan Yunusa Danzomo (Ma’aikatar Ilimi ), Dr Isah Yusuf Chamo (Ma’aikatar Ilimi mai zurfi, Kimiyya da Fasaha), Sagir Musa Ahmed (Ma’aikatar Watsa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu) da Hadiza Abdulwahab (Ma’aikatar Harkokin Mata).

Sauran sun hada da Col Muhammad Alhassan (mai ritaya) (Ma’aikatar filaye da tsare-tsare) Dakta Nura Ibrahim Dandoka (Ma’aikatar Muhalli), Gambo Shu’aibu Mallam (Ma’aikatar Ayyuka), Auwal Danladi Sankara (Ma’aikatar Ayyuka na Musamman). Musa Adamu Aliyu (Ma’aikatar Shari’a), da Muttaka Namadi (Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa).

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet