Connect with us

Labarai

Sojoji Sun Bukaci A Basu Dama Su Kakkabe ‘Yan Ta’adda Da Masu Laifi

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta sake yin afuwa ga ‘yan bindigar da ke addabar shiyyar Arewa maso Yamma na kasar nan ba,

Rundunar ta nemi gwamnoni su ba da dama don kawar da ‘yan ta’adda.

Rundunar ta gargadi masu aikata laifukan da su fice daga kasar nan take, inda ta ce za a yi musu cikakken hukunci, tare hana su shiga wasu sassan kasar idan suna yunkurin tserewa daga Arewa maso Yamma.

Shugaban hafsan sojin kasa, Manji janaral Taoreed Lagbaja, wanda ya bayyana hakan a shedkwatar rundunar da ke Abuja a lokacin da yake karbar bakuncin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

Ya yi kira ga gwamnan da su baiwa sojoji gudunmawa don kawar da duk wasu masu aikata laifuka.

“Mai girma gwamna, ina ganin muna bukatar mu duba wannan shirin na afuwa. Abubuwan da ke aikata laifuka sun tabbatar da cewa ba za a iya gyara su ba. Don haka batun yin afuwa ya samar da hanyar da za su sake haduwa su sake shiryawa da kaddamar da hare-hare,” inji Lagbaja.

Bayanin hafsan hafsan sojin ya biyo bayan kiraye-kirayen da tsohon gwamnan jihar, Sani Yerima ya yi a kwanakin baya na cewa a yi wa ‘yan bindiga afuwa.

Ya roki shugaban kasa, Bola Tinubu ya tattauna da ’yan ta’adda da ke aiki a jihar Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yammacin kasar nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet