Connect with us

Labarai

Wata Mata Ta Zuba Wa Yarinyar Abokiyar Zamanta Ruwan Zafi

Jami’an ‘yan sanda a jihar Ondo sun damke wata mai sayar da abinci kuma matar aure Misis Esther Godwin bisa zargin zuba ruwan zafi kan wata mata mai shayarwa Samuel Endurance kan zargin yin mu’amala da mijinta.

An kama Misis Godwin ne a karshen makon da ya gabata bayan ta zuba ruwa ga matar, Samuel, zuwa gidanta da ke unguwar Olofin da ke Idanre a karamar hukumar Idanre ta jihar.

Daily Trust ta tattaro daga majiya mai tushe cewa wadda ake zargin ta kira matar da ta ci mutuncin ta a waya da nufin ta zo ta karbi Mai.

Nan take matar da aka zubawa ruwan (Endurance) ta garzaya gidan domin karbar man tare da jaririnta tana sa ran wanda ake zargin zata mika mata da man.

Sai dai wani abin mamaki bayan wadda ake zargin bayan ta dauko man tare da jaririn ta, ta nemi jin alakar da ke tsakanin su da mijin ta.

An ce wacce ake zargin ta shiga dakinta, ta fito dauke da tankar ruwan zafi ta zuba a jikin Endurance.

Nan take aka garzaya da’ita zuwa cibiyar lafiya ta garin amma daga baya aka garzaya da ita babban asibitin Alade Idanre inda har yanzu take jinya.

Da take ba da labarin abin da ya faru a kan gadon rashin lafiya, Endurance ta bayyana cewa, duk da cewa ta kan yi aiki a gonar mijin da ake zargin, amma babu wani abu a tsakanin su face dangantaka ta ubangida da ma’aikaci.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, wadda ta tabbatar da kama wadda ake zargin ta ce za a gurfanar da ita gaban kotu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet