Featured
Abba K. Yusuf Ya Naɗa Sabbin Mukamai 14 A Hukumomi Da Ma’aikatu
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Dr. Farouq Kurawa amatsayin manajan darakta na hukumar bunƙasa aikin gona da raya karkara ta jihar Kano KNARDA.
Babban Sakataren yaɗa labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Laraba, ya ce gwamnan ya kuma naɗa wasu sauran mutane 13 muƙamai daban-daban na hukumomi da ma’aikatu.
Sauran mutanen da naɗa akwai Jarumin fina-finai Abba El-mustapha, amatsayin shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, da Engr. Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na hukumar KHEDCO, sai Alhaji Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari da Kaddarori na Jihar Kano KSIP, da Dokta Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da kayan Noma na Kano KASCO.
Sauran sune Hon. Sadiq Kura Muhammad, manajan darakta na gidan Zoo, da Injiniya Sani Bala, manajan daraktan hukumar lantarki a karkara, sai Hon. Shamwilu Gezawa, Hukumar Samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta Jihar Kano RUWASA, da Alhaji Tukur Bala Sagagi, Manajan Darakta na kukumar kula da yawon bude idanu ta Jihar Kano, da kuma Alhaji Yahaya Muhammad Idris manajan darakta na madaba’ar jihar Kano, yayin da Hon. Adamu Yahaya, ya kasance mataimakin manajan darakta.
Har ila yau akwai Dr. Muhammad S. Khalil, sakataren zartaswa na hukumar magance zaizayar ƙasa da kula da sauyin yanayi ta Jihar Kano KN-WECCMA, da Dokta Dahir M. Hashim, Jami’in hukumar ta WECCMA a Kano.
Sanarwar ta ce naɗin mukaman ya fara aiki nan take.
