Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Niger Zai Nada Mata 100 Mukamai A Gwamnatinsa

Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta baiwa mata mukamai 100 a cikin makon nan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar lauyoyin mata ta duniya (FIDA), karkashin jagorancin shugabar kungiyar Misis Bola Jibogun a gidan gwamnati dake Minna.

Bago ya ce nade-naden zai kasance ne domin cika alkawarin da ya dauka na daukar mata tare da aiwatar da manufofinsa da shirye-shiryensa.

Ya sanar da cewa daga cikin nade-naden 100, FIDA za ta samu ko-odinata da kuma manyan mataimaka na musamman guda biyu.

Gwamnan ya ba su tabbacin yin aiki tare da su don magance matsalolin da suka shafi jinsi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatinsa tana da tsare-tsare masu yawa ga mata da yara.

“FIDA na cikin wannan gwamnati don haka mu hada hannu mu hada karfi da karfe wajen kawo ci gaban jihar da ake bukata.

“Akwai shirye-shiryen mata da yawa, muna samar da gurabe da yawa don magance ayyuka masu inganci da kuma batutuwan da suka shafi jinsi a cikin wannan gwamnati kuma muna fatan hadin gwiwar za ta cimma buri na mata”, in ji shi.

Sakatariyar kungiyar ta FIDA, Safura Abdulkareem, ta bayyana cewa a matsayinsu na kungiya mai zaman kanta, suna kare hakkin mata da kananan yara tare da dakile duk wani nau’i na cin zarafin mata.

Ta bayyana shirin kungiyar na tallafawa gwamnati mai ci a jihar domin samun nasara.

A baya dai sakatariyar FIDA ta bukaci gwamnati mai ci ta hada hannu da kuma amincewa da ita don ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet