Connect with us

Ilimi

Jami’ar FUGUS A Zamfara Ta Kori Wasu Dalibai Bisa Wasu Laifuka

 

Hukumar gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Jihar Zamfara ta kori wasu dalibai sha uku (13) bisa samun su da laifin rashin da’a a jihar.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na Jami’ar Umar Usman ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Gusau, ya bayyana cewa an cimma matsayar ne a taron jami’ar karo na 82 da aka gudanar a ranar 5 ga watan Yulin 2023.

Ya bayyana cewa hukumar ta yi la’akari da rahoton da shawarwarin da kwamitin ladabtarwa na dalibai ya gabatar mata tare da korar dalibai bakwai, yayin da shida kuma aka dakatar da su bisa ga rashin da’a.

“Daliban da abin ya shafa an same su da laifuka daban-daban da suka saba wa doka da ka’idojin da suka shafi halin daliban Jami’ar.”

“Mukaddashin Sakataren Ilimi na Jami’ar, Malam Mu’awiyya Bello, ne ya gabatar da korar da kuma dakatar da daliban a ranar 7 ga watan Yuli, 2023 a madadin rijistarar jamai’a, Malam Yakubu Audu Anivbassa.”

Daliban da abin ya shafa sun fito ne daga sashin Cibiyar Ilimi, Business Administration, Microbiology, Economics, Science Education, Plant Science/Biotechnology, and Political Science. Wadanda aka dakatar sun samu hukuncin daga zangon karatu na daya zuwa na biyu.

“An hukunta daliban ne da laifuka daban-daban, da suka hada da sata, cin zarafi, yada bayanan da ba a tantance ba ta kafafen sada zumunta, da kuma rashin kokari a yayin jarabawa.”

“Wadannan laifukan sun ci karo da tanade-tanaden Sashen A, (xxv), Shafi na 62; Shafi na 68, (iv) akan Dokokin Gudanar da Halayen ɗalibai; da Sashe na L, Shafi na 69 – 73, (i– xxv) na Littafin dokokin ɗalibai.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet