Labarai
Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Wani Taron Gaggawa Da Gwamnoni
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ke jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzikin Najeriya.
Taron wanda aka fara ‘yan mintoci kadan da suka gabata a cikin zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, ya samu halartar kusan dukkanin gwamnonin jihohin kasar nan.
Taron ya kunshi gwamnonin tarayya 36, da Ministoci masu kula da harkokin kudi, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Babban Jami’in Kamfanin Mai na Nigeria National Petroleum Company Limited, NNPC, Mele Kyari, da dai sauransu.
Wadanda suka fara halartar zauren taron da aka shirya da misalin karfe 11 na safe sun hada da Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, da abokin aikinsa daga jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, da mataimakin gwamnan jihar Enugu, Barista Ifeanyi Ossai.
Haka kuma akwai, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawan; Katsina, Dikko Radda; Kwara, Abdulrahman Abdulrazak; Abia, Dr. Alex Otti; Chundung da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Sauran sun hada da Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; Delta, Sheriff Obrevwori; Kebbi, Nasir Idris; Anambra, Farfesa Charles Soludo; Edo, Godwin Obaseki; Mataimakin gwamnan jihar Kogi, David Onoja; Jihar Jigawa, Umaru Namadi; Jihar Yobe, Mai Mala Bunu; Bayelsa, Duoye Diri; Akwa Ibom, Umo Eno; Cross River, Prince Bassey Otu; Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa; Jihar Ogun, Dapo Abiodun; Jihar Sokoto, Ahmad Aliu; Jihar Filato, Caleb Mutfwang; Benue, Rev. Fr. Hyacinth Alia; da kuma Imo, Sanata Hope Uzodimma.
Idan ba a manta ba, kwamitin raba asusun tarayya na tarayya (FAAC) ya yi nuni da cewa ana sa ran gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi za su raba zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 1.95 a tsakanin su.
