Labarai
Mallakar Makamai Ba Bisa Ka’ida Ba: Za A Gurfanar Da Emefiele A Gaban Kuliya
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta sanya ranar 25 ga watan Yuli domin gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Kasa (CBN) Godwin Emefiele kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ne ya tsayar da ranar bayan cece-ku-ce a kan jinkirin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi na ganin laifin yana tare da umarnin kotuna daban-daban.
A ranar 13 ga watan Yuli ne dai hukumar SSS ta shigar da karar Emefiele kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
A cikin tuhume-tuhumen da hukumar SSS ta shigar a gaban kotu, ta zargi Emefiele da samunsa da bindiga guda daya mai lamba JOJEFF Magnum 8371 ba tare da lasisi ba.
An kuma yi zargin cewa ya mallaki harsashi guda 123 (harsashi) ba tare da lasisi ba.
Dukkan tuhume-tuhume biyun an ce sun saba wa sashe na 4 da 8 na dokar Cap F28 ta Dokokin Tarayya, na shekarar 2004, wadanda za a hukunta su a karkashin sashe na 27 (1) (b) (i) na dokar.
A wata zanga-zangar nuna rashin bin umarnin manyan kotuna da ke Abuja, wasu gungun lauyoyi a ranar 17 ga watan Yuli sun shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda suka nemi daure babban daraktan hukumar SSS, Yusuf Bichi a gidan yari bisa zargin raina kotu.
Lauyoyin, karkashin jagorancin Maxwell Opara da Ahmed Tijani a ranar Litinin din da ta gabata sun zargi Bichi da kin bin umarnin akan M. A. Hassan da Hamza Muazu da Bello Kawu da hukumar ta yi musu duk da umarnin da aka ba su.
