Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda A Kano Sun Gano Wasu Shanun Da Suka Yi Batan Kai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba da ke yawo a unguwar Ranka Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai a Kano ranar Lahadin nan.

Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Kiyawa ya ce, wani mutumin kirki ne ya ga shanun da suka bace a ranar 13 ga watan Yuli kuma ya ja hankalin ofishin rundunar ‘yan sanda na Hotoro.

“Mutumin kirkin ya shaida wa ’yan sanda cewa a kan hanyarsa ta zuwa Rakat Hotoro Quarters Kano, ya ga wasu shanu suna yawo sama da sa’o’i uku.

“Bayan samun rahoton, an tuntubi mazauna yankin kuma an kokarin gano masu shanun wanda hakan ya ci tura,” in ji shi.

Hakazalika sanarwar ta ce a ranar 14 ga Yulin 2023, wani mutum ya ba da rahoton ganin wata jaka wadda ake kyautata zaton ta fasinja ce da ya dauko a cikin baburin adaidaita sahu.

“An kai rahotan ne ofishin ‘yan sanda na Hotoro kuma duk kokarin da aka yi na gano mai ita lamarin ya ci tura,” in ji shi.

Sanarwar ta shawarci mazauna garin Kano da ke neman neman dukiyoyin da suka bata da su ziyarci ofishin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, a shedikwatar ‘yan sandan Kano, tare da shaidar mallakarsu. NAN

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet