Labarai
Kaduna: Wadanda Suka Mutu Sanadin Cutar Mashako Sun Karu
Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mashako a Kaduna ya karu zuwa 13 kamar yadda alkalumman hukuma suka nuna.
Rahoto ya nuna cewa mutane 10 sun mutu sakamakon cutar a Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna.
Yayin da yara 3 suka mutu a karamar hukumar Makarfi, yanzu haka wasu bakwai ke kwance a asibiti.
Da yake tabbatar da bullar cutar a karamar hukumar Markafi, sakataren lafiya na karamar hukumar, Malam Aliyu Alhassan, ya ce wadanda ake zargin sun kamu da cutar ne a unguwar Tashar Na Kawu da ke Unguwar Gubuchi a yankin.
Ya ce: “Wadanda abin ya shafa yara ne kuma an tura samfurin wadanda abin ya shafa Abuja domin a tantance su.
“An kai wadanda ake zargin suna dauke da cutar asibiti an kebe su don duba lafiyarsu kuma ana ci gaba da gano masu cutar domin kare ci gaba yaduwar cutar.”
Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ‘yan juhaf kan bullar cutar tare da umurtar ma’aikatar lafiya a jihar da ta tura tawagar gaggawa domin gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar matakin gaggawa, inji jaridar The PUNCH.
A halin da ake ciki, Babban Likitan cututtuka masu yaduwa na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna, Dokta Jeremiah Daikwo, ya koka kan yadda wasu al’ummar jihar ke kin yin allurar rigakafin cutar anthrax da ta barke a wasu jihohin.
Cutar bakteriya da ke addabar dabbobin gida da na daji da kuma ka iya kamuwa da mutane musamman kananan yara da watakila sun yi mu’amala da dabbobi masu dauke da cutar.
A wata hira da ya yi da manema labarai ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa mutane 17 ne suka kamu da cutar kuma “har yanzu muna ci gaba da bincike don gano karin mutanen da suka kamu da cutar.”
