Connect with us

Featured

Wasu Daliban Makarantar Sakandire Sun Lakadawa Malamin Su Duka Kan Hana Su Satar Jarrabawa

Wasu gungun daliban makarantar sakandire su 10 a jihar Ogun sun yi wa wani malami mai suna Kolawole Shonuga duka, wanda ya hana daya daga cikin su sata a lokacin jarrabawa.

Jaridar City & Crime ta rawaito labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata a Isanbi Comprehensive High School, Ilisan-Remo, da ke karamar hukumar Ikenne.

Wakilinmu ya tattaro cewa Shonuga, a yayin da yake duba jarabawar ajin SS1, ya kama wani dalibi, Ashimi Adebanjo mai shekaru 18 da yin satar jarabawa, kuma ya kwace takardarsa.

Bayan kammala jarabawar sa’o’i kadan, daliban suka yi dandazo, inda suka lakadawa Malamin nasu duka a kofar makarantar, kamar yadda shaidu suka shaida wa majiyarmu.

Daya daga cikin daliban, Kazeem Adelaja, ya bugi malamin akan sa, yayin da sauran suka lakada masa duka da hannayensu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Omotola Odutola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama dalibai 10 da ake zargi.

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kungiyar malaman makarantun sakandire (ASUSS) na jihar, Felix Agbesanwa, ya ce “al’amarin gaskiya ne kuma an sanar da ni. Matsayarmu ita ce, duk dalibin da ya daga hannu a kan malaminsa, to zai fuskanci fushin shari’a. Babu sauyi kan hakan. Kada dalibi ya daga hannu a kan malami, malami malami ne.”

Ya kara da cewa, “Na samu labarin an gurfanar da su gaban kotu.”

Gwamnatin jihar ta kuma yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da shan alwashin cewa ba za ta lamunci rashin da’ar da dalibai ke yi a fadin jihar ba.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin ilimi, kimiya da fasaha, Farfesa Abayomi Arigbabu, ne ya yi wannan gargadin a lokacin da yake karbar sabbin shugabannin kungiyar MAN.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet