Connect with us

Labarai

Nasarawa: An Dakatar Da Wani Shugaban Karamar Hukuma A Kano

Zababbun kansiloli takwas cikin 11 na karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano, sun amince da dakatar da shugaban karamar hukumar Lawal Shuaibu Aranfoso bisa zarginsa da bayar da hayar sashen kudaden shiga na karamar hukumar ga abokansa.

Sauran tuhume-tuhumen da ake yi wa shugaban dai sun hada da yin watsi da karamar hukumar gaba daya wajen biyan bukatunsa na kashin kai a Abuja da sauran wurare, lamarin da ya sa sakatariyar ta zama inuwar giginya.

Da yake magana a madadin sauran ‘yan majalisar, wani kansila da bai bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa tun bayan zabensa shugaban karamar hukumar ya yi watsi da karamar hukumar, kuma kusan ya koma Abuja da zama.

Ya bayyana cewa, a binciken da suka gudanar, sun gano wasu wuraren samar da kudaden shiga na karamar hukumar an bayar da hayar su ga wasu makusantan shugaban ba tare da sanin wasu wakilan karamar hukumar ba.

Ya kara da cewa, idan aka yi nazari sosai a kan karamar hukumar, wadda a da ta kasance cibiyar samar da kudaden shiga da ayyukan jin dadin jama’a, yanzu ya nuna cewa al’amura sun kasance cikin nadama.

“Mun kafa kwamitin bincike mai karfi wanda zai taimaka mana wajen gano yawan kudaden shiga da suka bace saboda abokansa da aka ba su hakin tattarawa ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.

“Muna kuma daukar dukkan matakan da suka dace don tallafa wa mutanen Nassarawa, wadanda ke matukar bukatar taimako daga gare mu,” in ji shi.

Duk kokarin da aka yi na tattaunawa da shugaban da aka dakatar, ciki har da aika masa da sakon kartakwana, ya ci tura domin ya ki amsa duk wata tambaya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet