Labarai
Tinubu Bai Aika Jerin Ministocinsa Majalisa Ba, Yayin Da Ya Rage Sa’o’i 48
Har yanzu dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai aika da jerin sunayen ministocin da zaba don nadawa ba wanda majalisar dattawa za ta amince kuma ta tantance.
Yayin da ya rage sa’o’i 48 kafin wa’adin ya kare bisa tanadin kundin tsarin mulkin Kasa.
A wani rahoto na musamman da Jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa Jinkirin da shugaban ya yi na gabatar da majalisar ministocinsa ya kara sa rai daga ‘yan Najeriya, wadanda ke dakon jerin sunayen ministocin da za su taimaka wa shugaban kasar wajen gabatar da ajandar sa ta sabon salon mulki.
Tinubu dai yana da lokaci har zuwa ranar Juma’a, 28 ga watan Yuli, don mika sunayen ga majalisar dattawa kamar yadda sashi na 42 (a) na kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa:
“Nadin kowane mutum a ofishin minista domin tabbatarwa sai majalisar dattawa za a yi cikin kwanaki sittin bayan ranar da aka rantsar da shugaban kasa”.
An rantsar da shi ne a ranar 29 ga Mayu.
‘Yan majalisar tarayya sun kuma ce suna jiran jerin sunayen ministocin daga shugaban kasa inda suka yi alkawarin tantance wadanda aka nada kafin su fara hutun shekara.
Akwai rahotannin da ke cewa jami’an tsaro da masu yaki da cin hanci da rashawa sun kammala binciken wadanda zaba don nada su kuma shugaban ya na gudanar da bincike na karshe a kansu.
Shugaban majalisar dattawa, Michael Opeyemi Bamidele, a jiya, ya bayyana cewa majalisar za ta karbi jerin sunayen ministocin da ake sa ran za a nada cikin sa’o’i 48 masu zuwa.
Da yake jawabi a wajen bikin cikarsa shekaru 60 da haihuwa da kuma gabatar da littafai jiya a Abuja, Sanatan ya ce da safiyar Talata ne Shugaba Tinubu ya shaida masa cewa ba zai samu damar halartar lakcar zagayowar ranar haihuwarsa ba saboda sakon da zai mika wa majalisar.
Bamidele, wanda ya yi aiki a matsayin babban mai taimaka wa majalissar dokokin Tinubu (SLA) a shekarar 1992 a lokacin da yake Sanata, ya ambato shugaban kasar yana cewa:
“Bari in gaya muku, ina bukatar in ba da kaina na tsawon sa’o’i 48 masu zuwa saboda dole ne a kawo wasikun majalisar dattijai, wasiku suna da matukar muhimmanci.”
Ya ci gaba da cewa: “Don haka, shugaban kasa ya roke Ni. Ya kamata mu gaya wa sauran ’yan Najeriya su yi addu’a don samun damar yanke shawara mai kyau ta yadda idan ‘yan Nijeriya suka ji jerin sunayen ministocinsa su ce eh yayi; wannan ba sabon abu ba ne, kuma yana tare da mu don yin addu’a ga mai girma shugaban kasa. Ya bukaci nisantar kowane irin tasiri.”
Makonni da suka gabata, an yi ta cece-kuce game da sunayen wadanda za a nada a matsayin ministoci amma Dele Alake, mai magana da yawun shugaban kasar, ya bayyana jerin sunayen da ake yadawa a matsayin cewa “kage ne kawai”.
