Connect with us

Labarai

Jami’an Tsaro Sun Cafke Barayin Wayar Lantarki A Filin Jirgin Saman MMIA — FAAN

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Kasa (FAAN) ta ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane uku da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne ta karkashin kasa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, ta hannun Abdullahi Yakubu-Funtua, daraktan hulda da jama’a da kuma karr hakkin kwastomomi na FAAN.

Sanarwar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a makarantar horas da ma’aikata a ranar Juma’a.

Ta ce, tawagar jami’an sintiri na sashen binciken laifuka da leken asiri na hukumar tsaron filim jiragen sama (CII), da kuma rundunar hadin gwiwa ta soja (JMTF) ne suka kama wadanda ake zargin.

Sanarwar ta ce “An kama biyu daga cikin wadanda ake zargin da misalin karfe 03:52 na dare yayin da suke tono da yanke igiyoyin wayar lantarkin da ke hada MMIA zuwa tashar cikin gida (MMA).

“Wanda ake zargi na uku, wanda ke zama barawon zaune tsakanin sauran mutanen biyu da ake zargi da saye a kasuwar Arena, Oshodi, an kama shi ne da misalin karfe 05:56, a tashar Hajj & Cargo bayan ikirari da sauran mutanen biyu suka yi.

“Binciken da ake ci gaba da yi ya nuna cewa an yanke wa daya daga cikin wadanda ake tuhuma hukuncin daurin kwanaki 28 a gidan yari saboda irin wannan laifin, wani lokaci a watan Afrilun 2022.

“A yanzu haka jami’an hukumar tsaro ta FAAN (AVSEC) suna yi wa wadanda ake zargin tambayoyi daga bisani za a mika su ga ‘yan sanda domin gurfanar da su a gaban kuliya.”

Idan dai za a iya tunawa a ranar 21 ga watan Yuli ne hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kama wasu da ake zargi da aikata irin wannan aika-aika.

Kafin haka dai FAAN ta sanar da cewa wasu da ake zargin barayi ne sun dauke na’urorin hasken wutar lantarkin da aka sanya kwanan nan a titin cikin filin (18L/36R) na MMIA a Legas.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet