Connect with us

Labarai

Hukumar PCACC Ta Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Hannu A Wata Almundahanar KASCO

Hukumar karbar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta fara bincike kan batan kudaden gwamnati daga kamfanin samar da ayyukan noma na Kano (KASCO) da suka haura Naira Biliyan hudu tare da kwace wasu manyan motoci da taraktoci.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka a ranar Asabar, a lokacin da ya jagoranci tawagar bincike zuwa rumbunan ajiye motoci da manyan motocin aikk da taraktoci da ake zargin an sayo da kudin da aka zaftare, a karamar hukumar Kumbotso ta jihar.

Rimin Gado ya ce an karkatar da kudaden ne daga kamfanin samar da kayan noma na Kano zuwa wata kungiya mai rijista da hukumar kula da harkokin kasuwanci (CAC) mai suna Association of Compassionate Friends.

“Kungiyar ta yi nufin ingantawa da kula da rayuwar ‘ya’yan marasa galihu a cikin al’umma, amma abin takaici sai aka mayar da ita hanyar satar dukiyar jama’a,” inji Shugaban.

Barista Muhuyi Rimin Gado ya bayyana cewa an ciro wadannan kudade ne daga asusun gwamnatin jihar Kano a matsayin tallafi ga hukumar KASCO amma an zaftare su ne ta hanyar amfani da wata kungiya mai rijista da sunan kasuwanci na kamfani.

“Mun kama mutane takwas da ake zargi kuma muna bincika sahihan bayanai ga hukumar.

Mutum guda daya daga cikinsu ya ce an ba shi wasu kudi ne domin ya yi karya a KASCO, amma ya ajiye kudin a gefe yana jiran wani lokaci kamar haka kuma ya mayar da kudin.”

“Ya zuwa yanzu mun kwato Naira miliyan goma sha biyar kuma mun yi nasarar toshe kusan Naira miliyan tamanin.”

Rimin Gado ya ce hukumar ba ta gamsu da yadda aka yi wasu hada-hadar kasuwanci tsakanin kamfanoni da wasu bankuna ba, yana mai jaddada cewa za a iya gayyato wasu manajojin bankuna don warware wasu batutuwa.

Ya kara da cewa hukumar za ta gurfanar da su gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar jihar musamman ma’aikatan gwamnati da su mika ingantattun bayanan da za su kai ga kwato kadarorin gwamnati da aka wawure, tare da ba su tabbacin basu kariya da kuma boye sunansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet