Labarai
Katsina: ‘Yan Sanda sun kama Amarya bisa zargin yanke wa ijinta Mazakuta
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke wa mijinta Azzakari.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, ASP Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da aka yi da shi a Katsina.
Ko da yake Aliyu bai bayyana sunan wanda abin ya afkawa ba, ya nuna cewa yana cikin mawuyacin hali a babban asibitin garin Malumfashi.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur.
Ya kara da cewa wadda ake zargin ta yi amfani da reza wajen aikata wannan mummunan aiki.
“Mun fara bincike kan lamarin.
“Amarya ce da ta haura shekara 30, watakila ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi aure, ko kuma ba aurenta ne na farko ba.
“Ba ni da cikakken bayani, za mu gano duk me ya janyo faruwar lamarin a bincikenmu,” in ji shi.
Aliyu ya kuma ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin girbar abinda da ta shuka bayan kammala bincike.
