Labarai
NLC A Katsina Ta Fara Gudanar Da Tattakin Zanga-Zanga
Mambobin kungiyar kwadago ta Kasa NLC reshen jihar Katsina a ranar Larabar nan sun bi sahun takwarorinsu wajen gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon wasu manufofin gwamnati na baya-bayan nan da suka hada da cire tallafin man fetur.
Mambobin kungiyoyi daban-daban ne suka hadu a shedikwatar NLC a jihar, da ke kan titin Kano.
An hada wannan rahoto ne a lokacin da suke shirin shiga zanga-zangar da ake gabatarwa a fadin Kasar nan.
A cewar shugaban NLC na Katsina, Hussaini Hamisu, tattakin za a fara shi ne daga shatale-talen Rolling Mill, da ke zagayen WTC daga nan za su fito.
Yayin da daga bisani za a koma shedkwatar NLC din inda zai yi jawabi ga jama’a.
Hamisu ya fayyace cewa matakin zanga-zangar na ranar Larabar nan za a yi shi ne don aikewa da sako kan wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.
Ya kara da cewa sauran matakan da za a dauka bayan zanga-zangar, shedkwatar kungiyar kwadago ta kasa za ta tantance bayan ta yi nazari kan rahotannin da sassan kungiyar daban-daban suka gabatar kan zanga-zangar.
Hamisu ya ce, “Tattakin na yau ana gudanar da shi ne a fadin kasar nan kuma jihar Katsina ta shiga.
“Shedkwatar kungiyar NLC ta kasa za ta tantance mataki na gaba da za a dauka bayan kowace jiha ta gabatar da rahotonta kan zanga-zangar kuma shedkwatar kasa ta yi nazarin rahoton.
“Ka sani, zanga-zangar yau ba yajin aiki ba ce. Ana son a aika da sako ne game da wahalhalun da talakawan Najeriya ke fuskanta sakamakon hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke a baya-bayan nan da suka hada da cire tallafin man fetur.”
Rundunar ‘yan sandan jihar ta baza wasu jami’anta a sassa daban-daban na babban birnin jihar ciki har da babbar hanyar shiga kungiyar NLC.
