Connect with us

Labarai

Hukumar Tace Fina-finai Da Dab’i Ta Fara Kama Masu Tallan Maganin Gargajiya

Shugaban Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Alh. Abba El-Mustapha ya jaddda aniyar sa ta kawo tsafta tare da gyara a bangaren masu tallan maganin gargajiya duba da yadda wasun su ke yada kalaman batsa da hotunan da basu dace ba da nufin tallata magungunan su dan su ja hankalin masu siya.

El-Mustapha ya Kara da cewa shugabancin sa ba zai zubawa wannan halayya ido ta cigaba da faruwa a cikin alumma ba.

Wannan na kunshe ciki wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a nu hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Asabar din nan.

Ya ce amfani da kalaman batsa ya sabawa tarbiyar jihar Kano tare da koyarwar addinin Musulinci.

Abba na yin wannan jawabi ne a gaban harabar hukumar tace Fina-finan ta jihar, jim kadan bayan kammala aikin kaman masu maganin gargajiyar da aka samu da laifin saba dokar hukumar a wani aikin hadin gwiwa data gudanar tsakanin jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar tace Fina-finan ta Kano.

Alh. El-Mustapha yace doka ce tabawa hukumar damar gudanar da wannan aiki don haka hukumar zata yiwa dokar biyayya sau da kafa domin cimma nasarar da tasa a gaba.

Idan ba a mantaba sati biyu da suka gabata, hukumar ta soke lasisin gudanar da aiki ga dukkannin abokan huldar ta, sannan tace har sai ta tantance su tare da basu damar cigaba da aiki ciki kuwa harda Kungiyar masu tallan maganin gargajiyar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet