Connect with us

Labarai

Cikin Wata 6 Hadarin Mota Ya Yi Sanadin Rasa Rayukan Mutane 4,387 – FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta tarayya Kasar nan ta ce mutane 4,387 ne suka mutu sakamakon hadurran ababen hawa daga watan Janairu zuwa Yunin bana a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.

Jami’in hulda da jama’a na na rundunar Marshal, Mista Bisi Kazeem, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ranar Lahadin nan a Abuja.

“Daga watan Janairu zuwa Yuni, jimillar mutane 4,387 ne suka mutu sakamakon hadurran da suka yi a kan tituna. Rundunar ta kuma tattara masu raunuka 14,108 daga hadurran a cikin watannin.

“Wadannan hadarurrukan sun faru ne sakamakon tafiye-tafiyen dare, gajiya, keta hanya, gudun wuce gona da iri, amfani da tayoyin da wa’adinsu ya kare.

“Kuma kun san jami’an ba sa aiki da daddare, domin irin wadannan direbobin suna amfani da rashin zuwanmu da daddare don karya ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa,” in ji shi.

Kazeem ya ce daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa wadannan hadarurruka shi ne, galibinsu direbobi ne da ba su da horo ko kuma wadanda ba su da kwarewa.

Ya ce an gano hakan ne ta hanyar bincike mai zurfi na hukumar.

“Kafin yanzu, babban batun shi ne rashin iya cika ka’idojin tuki cikin aminci.

“Wannan ya sa aka kafa doka a kan tanka don tabbatar da cewa kafin duk wata tankar dakon kaya dole ne ta cika ka’idojin aminci.

“A halin yanzu, za mu iya cewa matakin yarda, musamman na na’urorin kayyade gudu duk da cewa bata da kashi 100 amma yana da ban sha’awa sosai,” in ji shi.

Ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da wayar da kai kuma an shirya gudanar da ayyukan sintiri na musamman a tsakankanin lokacin domin yin bita ga.masu motocin da ba su bi ba.

Kazeem ya kuma ce hukumar ta samu adadin masu raunuka 14,108 daga hadarurrukan tare da ceto mutane 15,789 da basu ji rauni ba a hadarurrukan kan hanya a lokacin.

Ya ce ba a samu karuwar hadurran motoci da manyan motoci da tankokin ba, sai dai an samu koma baya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet