Connect with us

Featured

Kano: Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da Gadaje 86 a Asibitin Yara na Hasiya Bayero

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake buɗe Asibitin yara na Hasiya Bayero Paediatric Hospital.

Da yake jawabi yayin buɗe Asibitin, Gwamna Abba Kabir ya zargi gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje da sayar da Asibitin, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin wahala.

A cewar sa, hakan ta sanya ya ci alwashin idan ya zama gwamnan Kano sai ya ƙwato wa al’umma kayan su.

“Duk da irin roƙon da al’umma su ka riƙa yi, amma gwamnatin da ta gaba ta sayar da wannan asibiti. Hakan ya sanya al’umma suka rika shan wahala. Dole su ka riƙa zuwa neman Asibitocin yara masu tsada kuma ba lallai suna da ingancin wannan ba.

“Da mu ka ga haka, sai mu ka ci alwashin kwatowa al’umma asibitin su. Yau ga shi mun cika alƙawari. Mu na cikin farin ciki da alfahari da wannan gagarumin aikin,” in ji gwamna Abba.

Ya ce Asibitin yana ɗauke da gadaje 86, kuma an saka masa kayayyakin aiki na zamani da za a rika kula da lafiya cikin inganci da sauƙi.

Ya kuma ja kunnen jami’an lafiya na Asibitin da su kula da gudanar da ayyukan su, inda ya gargaɗe su a kan yin fashi da makara, inda ya ce “gwamnati ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.”

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da ya yi na sake buɗe Asibitin.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet