Connect with us

Labarai

Jam’iyyar NNPP Kano Ta Musanta Labarin Dakatar Da Kwankwaso

A wani sauyi da aka samu shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dunguruwa ya bayyana labarin dakatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a matsayin labaran kanzon kurege.

Da yake zantawa da jaridad NIGERIAN TRIBUNE ta wayar tarho daga Abuja, Dungurwa ya ce yana wajen taron majalisar zartarwar jam’iyyar ya ce ba a yi irin wannan yunkuri ba.

“A yanzu haka ina Abuja inda shugabannin jam’iyyar ke gudanar da taro, babu wani abu makamancin haka.”

Shugaban NNPP ya kara da cewa, “Muna wajen taron Majalisar Zartaswa ta kasa (NEC) a Abuja, mun kada kuri’ar amincewa da Dokta Kwankwaso.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin amintattu ya kara wa shugaban riko da sakatariyar jam’iyyar wa’adin mulki.

Ya kara da cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Sanatoci, zababbun ‘yan majalisar wakilai da zababbun ‘yan majalisar dokokin jiha sun amince da taron kwamitin amintattu tare da kada kuri’ar amincewa da Dr Kwankwaso.

Jaridar Primetime ta rawaito Rahoton kwamitin, a safiyar ranar Talata, ya ce kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP ya dakatar da dan takararta a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Kamfanin dillancin Labarai Kasa NAN ya ruwaito cewa dakatarwar na tsawon watanni shida ne.

NAN ta ruwaito cewa mambobin jam’iyyar ne suka kada kuri’ar amincewa da dakatarwar a babban taronta na musamman, wanda aka gudanar a otal din Rockview da ke Apapa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet