Connect with us

Labarai

Jigawa: Wasu Da Ake Zaton Barayi Ne Sun Sace Kayayyakin Da Kudinsu Ya Kai N20m – Kwamishina

 

Wasu da ake zargin barayin shanu ne sun kai hari a matatar ruwa ta Birninkudu da ke karamar hukumar Birninkudu a jihar Jigawa.

Barayin wanda suka lakada wa ma’aikata duka, tare da sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Ibrahim Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar a ranar Juma’ar nan.

Garba, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya ce gwamnati za ta dauki tsauraran matakai a kan masu yin zagon kasa ga kokarinta na samar da ruwan sha ga mazauna jihar.

“Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske. ‘Yan fashin sun sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.

“Wannan shi ne karo na farko da hakan ya faru tun lokacin da aka samar da wannan wurin ruwa a Birninkudu cikin shekaru 50 da suka gabata.

“Hakan na faruwa a fadin jihar kamar yadda ya faru a Kazaure inda aka lalata rijiyoyin burtsatse kusan 20, aka tona wayoyin wuta aka kwashe su.

“Haka kuma ya faru a Babura, Gumel da Dutse. Don haka abin yana faruwa sosai,” Garba ya koka.

Ya kara da cewa yawaitar sata da lalata wuraren samar da ruwa a fadin jihar na janyo wa ‘yan jihar wahalar samun ruwan sha tare da kawo cikas ga kokarin gwamnati na samar da ruwan sha ga kowa da kowa.

Don haka kwamishinan ya shawarci jama’a da su kula da duk wasu muhimman ababen more rayuwa da cibiyoyin gwamnati ke samarwa a yankunansu tare da kai rahoto ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.

Shima da yake magana, Manajan shiyyar na Hukumar samar da Ruwa ta Jigawa mai kula da Birninkudu, Buji da Gwaram, Malam Yunusa Shuaibu, wanda yana cikin wadanda ake zargin barayin ne suka kai masa hari, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai hari a cibiyar da tsakar daren ranar Talata.

“A ranar Talata da tsakar dare ne wasu gungun mutane kimanin 10 dauke da muggan makamai suka kai hari a wurin da ni da manaja da wasu ma’aikata biyu suka tarar kuma suka farmake mu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet