Connect with us

Labarai

Kungiyoyin Fararan Hula A Nijar Sun Yi Zanga-Zangar Neman Sojojin Faransa Su Fice

Jamhuriyar Nijar ta ba da kwarin gwiwa a ranar Juma’ar a wani mataki na gudanar zanga-zangar adawa da Faransa a karshen mako, a daidai lokacin da rikici ke kara tsami tsakanin sabbin shugabannin mulkin sojan kasar da abokan kawancen ta na gargajiya.

Gamayyar kungiyoyin farar hula da ke adawa da kasancewar sojojin Faransa a Nijar sun kira zanga-zangar zaman dirshan na kwanaki uku, daga yau Juma’a.

Zanga-zangar wadda kungiyar M62 ta shirya za ta gudana ne a tsakiyar birnin Yamai domin neman ficewar sojojin Faransa.

Faransa dai na da dakaru kusan 1,500 a Nijar, kuma yawancinsu suna jibge a wani sansanin sojin sama dake kusa da babban birnin kasar, wadanda aka tura domin su taimaka wajen yaki da ‘yan tada kayar baya.

Za a fara ranar Asabar, za a ci gaba da “har sai dukkan sojojin Faransa sun fice”, in ji masu shirya zanga-zangar.

Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ta tabarbare ne tun bayan hambarar da shugaba Mohamed Bazoum, wanda wasu ke zargin da hannun Faransa a juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli.

Paris ta damu akan Bazoum kuma ta ki amincewa da sabbin masu mulki a yankin Sahel mai fama da rikici.

Rikicin ya yi zafi a wannan makon lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta tube jakadan Faransa daga kariyar diflomasiyya tare da ba da umarnin ‘yan sanda su kore shi, a cewar wata wasika da kamfanin dilancin labaren AFP ya gani a ranar Alhamis.

Tuni dai hukumomin kasar suka bai wa wakilin Faransa Sylvain Itte wa’adin sa’o’i 48 da ya bar kasar a ranar Juma’ar nan.

Faransa ta ki amincewa da matakin, tana mai cewa gwamnati ba ta da hurumin yin irin wannan umarni.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Kakakin sojin Faransa Kanar Pierre Gaudilliere a ranar Alhamis ya yi gargadin cewa “Rundunar sojan Faransa a shirye suke da su dau mataki ga duk wani tashin hankali da zai iya cutar da ofisoshin diflomasiyya da sojojin Faransa a Nijar”.

“An dauki matakan kare wadannan wuraren,” in ji shi.

A ranar alhamis din da ta gabata ne jami’an tsaro suka yi wa motocin da suka fito daga ofishin jakadancin Faransa da ke jamhuriyar Nijar binciken kwakwaf, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa AFP.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet