Labarai
Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe N3.7bn Domin Siya Da Raba Kayan Tallafi
A ci gaba da kokarin dakile radadin cire tallafin man fetur ga mazauna yanki, gwamnatin jihar Sokoto ta ware kimanin Naira biliyan 4 kan kayayyakin abinci da za a raba a fadin kananan hukumomi daban-daban.
Da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisa bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jiha a ranar Juma’a, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Dr Jabir Maihula, ya ce gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da sayen kayayyakin da za a raba.
A cewar kwamishinan, “Mambobin majalisar zartaswar jihar a taronsu na farko sun amince da sayen buhunan shinkafa 57,000 mai nauyin kilogiram 50 a kan kudi Naira biliyan 2.508.
“Majalisar ta kuma amince da siyan wasu buhunan gero 26,000 mai nauyin kilogiram 100 akan kudi Naira biliyan 1.430.”
Ya ce kayayyakin sun kuma hada da wasu buhunan masara 44,000 da gwamnatin jihar za ta saya tare da gwamnatin tarayya.
Ya bayyana cewa duk da haka gwamnan zai kafa kwamitin da zai sanya ido kan yadda ake raba kayan abincin a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.
A halin da ake ciki, domin saukakawa mutane a fannin sufuri, majalisar zartarwa ta jihar ta kuma amince da siyan motocin Toyota Hiace mai kujeru 50, samfurin 2022 mai kujeru 18 kan kudi Naira biliyan 2.8.
Ta kuma ware sama da Naira miyan 560 domin siyan mota kirar Toyota Camry guda 20, samfurin 2022, da nufin samar da saukin sufuri ga mata a jihar.
Kwamishinan harkokin addini na jihar ya ci gaba da bayanin cewa, motocin za kuma su samu tallafin wasu motocin bas guda 10 da kungiyar BUA ta baiwa jihar kwanan nan.
