Connect with us

Labarai

Shugaban Kasa Tinubu Zai Halarci Taron G-20 A Birnin Dalhi

Shugaban Kasar Najeriya Ahmad Bola Tinubu zai halarci taron kasashen G-20 da zai gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya.

Babban burin Tinubu a taron shi ne jawo jarin kasashen waje zuwa Najeriya daga sassa daban-daban na duniya don tallafawa ci gaban kayayyakin more rayuwa a kasar.

Taron na da nufin tinkarar manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya da daidaiton kudi na kasa da kasa.

Shugaba Bola Tinubu na shirin halartar taron kasashen G-20 da zai gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.

Ngelale ya bayyana cewa babban burin Tinubu a taron shi ne jawo jarin kasashen waje zuwa Najeriya, yana mai jaddada muhimmancin tara jari masu zaman kansu daga sassa daban-daban na duniya don tallafawa ci gaban kayayyakin more rayuwa a kasar.

G-20, wanda kuma ake kira Rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, taron gwamnatoci ne da ya kunshi kasashe 19 da Tarayyar Turai.

“Ana da nufin tinkarar manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya, kamar daidaiton kudi na kasa da kasa, rage sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa.

Kungiyar ta kunshi kasashen Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Koriya ta Kudu, Japan, Mexico, Rasha, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Burtaniya, Amurka, da kuma Tarayyar Turai.

Ngelale ya kara da cewa, an shirya shugaba Tinubu zai tattauna da shugabannin duniya, shugabannin kasashe, shugabannin masana’antu, da manyan jami’an fitattun kamfanoni, musamman wadanda suka samo asali daga kasar Indiya.

“Za mu tabbatar da cewa, a karkashin jagorancin shugaban kasa, mun yi amfani da damar da muka samu wajen kara wa al’umma kimar kasa, da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, da kuma kara habaka da samar da albarkatu domin al’ummar kasar nan su lamunce cewa gwamnati za ta iya samar da kudade yadda ya kamata tare da tallafawa shirye-shiryenta na gaba.

“Akwai abubuwa da yawa da za mu iya kawowa, kuma idan muka shigo Najeriya a mako mai zuwa, za a rika samun labarai kai tsaye daga Indiya, wadanda zan samar da su a kowace rana don baiwa ‘yan Najeriya cikakkiyar damar sanin abin da shugabansu ke yi a madadinsu,” inji shi. .

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet