Connect with us

Labarai

Kotu Ta Daure Mutane 8 Bisa Samunsu Da Laifin Zamba A Sokoto, Da Abuja

Akalla mutane takwas ne aka yankewa hukunci tare da dauresu bisa laifin zamba a Sokoto da Abuja.

Mai Shari’a M.U. Dogondaji na babbar kotun jihar Sokoto ya yanke wa biyu daga cikin wadanda ake zargin, Sanni Dikko da Naabu Umar hukunci, bisa laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma aikata zamba cikn aminci.

Dikko dai ya hada baki da Umar wajen karbar kudi naira 1, 500,000 daga hannun wanda ya kai kara mai suna Mustapha Mudashir a wani cinikin fili.

“Bincike ya nuna cewa Dikko, a baya ya sayar da fili ga wani Ashiru Muhammed, ya sa Umar ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki filin domin ya shawo kan Mudashir ya sayi kadarar kan kudi Naira miliyan 1.5.

“Mudashir yana cikin aikin ginin filin ne a lokaci sai ainihin mai filin ya dakatar da shi.

“Mai shari’a Dogondaji ya yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ko kuma zabin tarar Naira 200,000 kowanne.

“An kuma umarce su da su biya N1, 500,000 a matsayin diyya ga wanda aka zambata ta hanyar EFCC ko kuma su iya fuskantar daurin shekaru biyar a gidan yari,” in ji wata sanarwa a shafin Facebook na EFCC ranar Juma’a.

Haka kuma, Mai shari’a O. I. Adelaja na babbar kotun birnin tarayya da ke Kubwa, a Abuja, a ranar Alhamis, ya yanke wa wasu mutum shida hukunci bisa tuhuma guda daya ta zamba a Intanet.

Wadanda aka yankewa hukuncin su ne Anekwu Peterdamian, Eta Okang, Kolawole Taiwo, Ohue Daniel, Ocholi Husseni da Olatunji Johnson.

Sanarwar ta EFCC ta kara da cewa, “Mai shari’a Adelaja ta yanke wa Anekwu hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari tare da zabin tarar N2m. Haka kuma zai bada diyyar dala 4,000 da mota kirar Mercedes Benz CLA 250 da wayoyi ga gwamnatin tarayya.

“Eta ta kama shi shekaru biyu a gidan yari ko kuma tarar N2m. Bugu da kari, zai bada diyyar ga gwamnatin tarayya ta dala $4150, wayoyin hannu da kwamfutar tafi-da-gidanka.

“Ohue, Ocholi da Olatunji sun fuskanci hukuncin zaman gidan yari na shekara daya kowanne tare da zabin tarar N500,000, yayin da Kolawole ya samu hukuncin da ba na tsarewa ba.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet