Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Gana Da Masu Makarantu Masu Zaman Kansu Kan Wata Manhaja

Gwamnatin jihar Kano ta wayar da kan masu makarantu masu zaman kansu kan wata sabuwar manhaja da ta kera don inganta ayyukansu da kuma samar da bayanan masu kyau.

Da yake jawabi a wajen taron wayar da kan jama’a, a ranar Asabar, mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan makarantu masu zaman kansu da na sa kai, Alhaji Baba Abubakar Umar ya ce makasudin taron shi ne wayar da kan masu makarantu masu zaman kansu kan yadda ake amfani da sabbin manhajoji da kuma fahimtar juna kan dalilin da ya sa gwamnati ta fitar da wasu manufofi kan makarantu masu zaman kansu.

“Kusan makonni uku baya, mun fitar da fom din tabbatarwa kyauta ga masu makarantu masu zaman kansu, ta yadda gwamnatin jihar za ta samu bayanan ilimi domin wasu dalilai na tsare-tsare.”

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Baba Umar ya ce akwai bukatar gwamnati ta san irin ayyukan da masu gudanar da makarantu masu zaman kansu suke yi da kuma tsaftace fannin domin samun ingantaccen ilimi.

“Ba gwamna ne ya nada ni domin in farauto masu makarantu masu zaman kansu ba amma don in hada ku don inganta fannin,” in ji Umar.

“Mun samar da wata manhaja da za ta iya daukar bayanan duk ma’aikata, wanda shi ne na farko a Najeriya wanda zai iya bada duk bayanan da ake bukata ga kowace gwamnati don tabbatar da gudanar da ayyukan makarantu masu zaman kansu.”

“Don haka wannan taron wayar da kan jama’a shi ne masu makarantu masu zaman kansu su fahimci dalilin da ya sa muka ce za su zama abokan gwamnati da kuma dalilin da ya sa gwamnati za ta zama aminan su.

A nasa bangaren, Abdullahi Muhammad Abdullahi wanda daya ne daga cikin wadanda suka kirkiri manhajar, ya ce manhajar wata hanya ce da ta samar da cikakkiyar hanyar sadarwa ga masu makarantu da sauran jama’a domin mu’amala da hukumar kula makarantu masu zaman kansu da na sa kai a jihar Kano.

Ya kara da cewa tana bayar da albarkatun ilimi wadanda suka dace da tabbatar da bin manufofin jihar Kano kan ilimi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet