Labarai
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Fashi A Wani Banki, Sun Kama Mutum Guda
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta dakile wani yunkurin fashi da makami a wani banki da ke daura da Estate Maplewood, a Oko Oba, da ke jihar Legas.
Wadanda ake zargin dai sun fasa kofar tsaron shiga bankin yayin da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar suka mamaye wurin domin daidaita lamarin.
An dakile fashin kuma an kama wani da ake zargi.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce “Mun samu kiran wayar gaggawa ne da karfe 4:20 na safe kuma muka amsa cikin gaggawa.
“Zuwa yanzu tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Legas aiki ne da ba za mu yi kasa a gwiwa da shi ba”.
