Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Dauki ‘Yan Banga 7,000 Domin Magance Matsalar Tsaro

Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matasa 7,000 aikin binilanti domin sintiri a jihar saboda kara kaimi ga kokarin da hukumomin tsaro na tarayya ke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Gwamna Uba Sani da yake jawabi a lokacin da aka fara horas da sabbin ‘yan bijilantin da aka dauka a kwalejin ‘yan sanda ta Kaduna.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an dakile matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran laifukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ‘yan jihar.

Dubban matasa maza da mata da suka taru a kwalejin ‘yan sanda da ke babban birnin jihar an fito da su ne daga kananan hukumomin jihar 23.

A cewar gwamnan, za a tura ‘yan bangar zuwa yankunan karkara na jihar.

Daukar ma’aikata da tantance wadanda aka horas na tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin kananan hukumomi da shugabannin gargajiya da na addini.

Gwamna Sani ya yi imanin cewa, wannan shiri wani babban mataki ne na maido da tsaro da ci gaba a jihar, zai kuma samar da ayyukan yi ga matasan.

A yayin da take fuskantar kalubalen rashin isassun ma’aikata wajen samun nasarar yaki da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a cikin al’umma.

Don haka gwamnatin jihar Kaduna ta yi fatan daukar wadannan mata da maza a aikin sintiri na jihar zai taimaka wa jami’an tsaro na al’ada tare da basirar aiki saboda iliminsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet