Connect with us

Labarai

Rashin Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Wasu Manyan Kasuwannin Shanu

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu da aka fi sani da Kara a kananan hukumomi biyar na jihar nan take.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Zamfara, Alhaji Mannir Haidara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Lahadi.

A cewar Haidar, kasuwannin shanun da abin ya shafa sun hada da Danjibga da Kunchin-Kalgo a karamar hukumar Tsafe, da kasuwannin shanu na Bagega da Wuya a karamar hukumar Anka, da Dangulbi da Dansadau a karamar hukumar Maru, Dauran a karamar hukumar Zurmi, da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.

Ya ce rufe kasuwannin shanun na wucin gadi ya biyo bayan taron kwamitin sulhu ne.

“Wannan wani bangare ne na matakan magance matsalolin tsaro a jihar. Gwamnati ta lura da yadda ake saidawa da lodin satar shanu da ake zargin ‘yan bindiga ne a kasuwannin da abin ya shafa,” in ji Kwamishinan.

Don haka gwamnati ta yi kira ga hukumomin tsaro da hukumar kula da lafiyar dabbobi da kiwo ta jihar da su tabbatar da bin matakan da suka dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet