Connect with us

Labarai

Gwamnan Niger Ya Bayyana Kaduwarsa Bisa Rasuwar Mutane A Hatsari Kwale-kwale

 

Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana kaduwarsa game da hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Gwamnan ya nanata muhimmancin amfani da rigunan tseratar da rai na ruwa yayin hawa kwale-kwale.

Gwamnan ya kuma gargadi mazauna jihar da su daina yin cunkuso lokacin hawa kwale-kwalen.

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana kaduwarsa dangane da hatsarin kwale-kwalen da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a al’ummomin da ke tsakanin Jebba da Kainji Dam a karamar hukumar Mokwa a jihar.

Bago, wanda ya yi magana a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim, ya fitar, ya nanata muhimmancin amfani da rigunan tsira yayin hawa kwale-kwalen.

Gwamnan ya kuma gargadi mazauna garin da su daina cunkusuwa wajen hawa kwale-kwale.

Bago ya bayyana lamarin a matsayin mummuna kuma wanda ba a so.

“Wannan lamari ne mai ban tsoro da ban tausayi ga mutanen al’ummomin da abin ya shafa kuma ina cikin bakin ciki. Ina addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su a Aljannah Firdausi,” inji gwamnan.

Da yake jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, Bago ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja da ta yi duk abin da ya kamata domin rage radadin da jama’a ke ciki.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma baiwa wadanda suka jikkata sauki cikin gaggawa.

An tattaro cewa kwale-kwalen yana jigilar mutane sama da 100 daga yankunan da ke makwabtaka da su zuwa Sabon Matsugunin Gbajibo lokacin da ya kife.

Ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 26, galibi mata da yara, yayin da aka ceto sama da mutane 30.

Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto hadin gwiwa tsakanin ‘yan sandan ruwa da masu ruwa da tsaki na cikin gida tare da hadin gwiwar hukumar NSEMA.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet