Connect with us

Labarai

‘Yan Sandan Kano Sun Ja Hankalin Mazauna Yankunan Da Za Su Ji Karar Harbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Lahadi da daddare ta ja hankalin mazauna unguwannin da ke kusa da kwalejin horas da jami’an kwastam da ke Goron Dutse da kada su firgita saboda karar harbe-harbe da za su ji nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa kwalejin horon na gudanar da atisayen harbi na kwanaki bakwai.

“CP Mohammed Usaini Gumel yana sanar da jama’a cewa ma’aikatan kwalejin horas da jami’an kwastam ta Kasa, da ke Goron Dutse a Kano za su gudanar da atisayen harbi na kwanaki bakwai a Hawan Kalibawa, da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano.

“Za su gudanar da atisayen ne daga ranar Litinin 11 ga Satumbar 2023 zuwa Lahadi 17 ga Satumbar 2023 daga 06:00 na safe zuwa 18:00 na yamma kullum.”

Don haka, CP ya shawarci jama’a musamman mazauna kauyukan Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalama da ke cikin karamar hukumar Dawakin Tofa/Ungogo da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe amma su nisanci wurin har sai atisayen ya kammala.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet