Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Gwale
Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso
Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin mai kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu da majalisar tayi
Shugaban karamar hukumar zai ci gaba da zama dakatacce har sai an kammala bincike
Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso na tsawon watanni uku.
Majalisar ta amince da rahoton kwamitinta mai kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu a zamanta na ranar Talata, bayan da aka gabatar da zarge-zargen ga shugaban na sayar da filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Majalisar ta ce mutum shida daga cikin kansilolin, wakilai 10 ne suka kai karar sa zuwa ga majalisar kan halin da shugaban ya ke ciki.
A cewar kakakin majalisar dokokin jihar, Jubril Ismail Falgore, an kuma zargi shugaban karamar hukumar da yanke shawara ta bai daya ba tare da daukar ta kansilolin ba.
Don haka ne majalisar ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai binciki zargin sannan ya bayar da rahoto nan da watanni biyu sannan ta umarci mataimakin shugaban karamar hukumar da ya karbi ragamar tafiyar da harkokinsa na tsawon watanni uku, har sai an kammala bincike.
