Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano Ya Dakatar Da Manajan Daraktan KASCO Kan Zargin Almundahana

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayar da umarnin dakatar da Manajan Daraktan Kamfanin Samar da kayayyaki aikin noma na Kano (KASCO) Dakta Tukur Dayyabu Minjibir.

An dakatar da Manajan Darakta ne bisa zarginsa da hannu wajen sayar da hatsi mallakin Gwamnatin Jihar Kano.

Umurnin da Gwamnan ya bayar na daga cikin jajircewar sa na rashin hakuri idan aka aikata laifin cin hanci da rashawa a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai a ranar Larabar nan.

A cewar Bature, Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin dakatarwar ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Satumbar 2023 wanda sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya mika.

Jaridar Kakaki ta rawaito cewa An umurci Dakta Dayyabu da ya mika al’amuran kamfanin ga babban jami’i na gaba nan take har sai an kammala bincike.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet