Connect with us

Labarai

Edo: An Garkame Wa Mataimakin Gwamna Kofar Shiga Ofishinsa Na Gidan Gwamnati

Rikicin tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, ya dauki sabon salo a ranar Litinin din nan bayan matakin da gwamnan ya dauka na hana mataimakinsa shiga gidan gwamnati.

Shaibu ya samu kaduwa a lokacin da ya isa ofishinsa ranar litinin, ya tarar da kofar ofishin mataimakin gwamna da babbar kofar shiga gidan da sarkoki da manyan makullai.

Yayin da shi da mukarrabansa suka jira na kusan sa’a guda kafin su tafi, Shaibu, a tsawon lokacin rahotanni sun nuna cewa sun yi matukar kokarin ganin sun isa wurin gwamnan amma abin ya ci tura.

Wani mai taimaka wa mataimakin gwamnan da ya bayyanawa jama’a wadannan hotunan da aka sakaya sunansa ya bayyana cewa shugaban nasa ya tattauna da kwamishinan ‘yan sanda da daraktan ma’aikatan jihar inda ya sanar da su yadda aka hana shi shiga ofishin sa.

A cewarsa, babu wata sanarwa a hukumance da ta nuna cewa an kulle ofishin mataimakin gwamnan.

Don haka an ce Shaibu ya gayyaci kwamandan sansanin da ke gidan gwamnati, SP Ibrahim Babatunde, inda ya tambaye shi dalilin da ya sa aka garkame ofishinsa.

“Ya ce umarni ne daga sama ya kara da cewa CSO a gidan gwamnati, Wabba zai yi bayani,” in ji mataimaki.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, An ce Shaibu ya yi kira ga Wabba Williams wanda ya yi alkawarin zuwa wurin, amma bai zo ba duk tsawon lokacin da Shaibu ya dauka yana jira.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet