Connect with us

Labarai

FG, Gwamnatin Niger, Da IFAD Za Su Kashe Miliyan 87.1 Don Bunkasa Noman Shinkafa

Gwamnatin jihar Niger haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da IFAD sun amince da kashe zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 87.1 domin bunƙasa noman shinkafa.

Za a yi shirin ne a tsakanin manoma masu noman rani na jihar a wannan shekara ta 2023.

Ko’odinetan Shirin International Fund for Agricultural Development wato IFAD Dr. Mathew Ahmed ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai jim kadan bayan ziyarar ban girma da ya kai wa kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar a Minna.

Mathew Ahmad Ya bayyana cewa Gwamnatin ta dauki matakin ne domin baiwa manoma da dama a yankunan karkara damar cin gajiyar shirin don bunkasa noma da inganta rayuwar manoma a jihar.

Tun da farko Tawagar ta IFAD ƙarƙashin Jagorancin Dr. Samuel Eremie a ziyarar ban girman ta koka da yadda Gwamnatin Jihar Neja ke biyan kuɗaɗen takwarorinta duk da dimbin alfanun da aka samu daga shirin a jihar.

Ya kara da cewa, “Akwai buƙatar a gaggauta bin diddigin kuɗaɗen da takwarorinsu na IFAD ke bayarwa don gudanar da ayyukan IFAD ɗin. “Tallafin da Jihar ke samu yayi ƙasa sosai kuma ƙalubale ne akan mu, kuma muna addu’ar Allah ya kawo mana canji, abin mamaki ne a gare mu yadda Jihar Neja ta samu nasarori a harkar noman shinkafa duk da ɗan abinda take samu ba wani bane”.

A halin da ake ciki kwamishinan noma da albarkatun kasa na Jihar Musa Salihu Bawa Bosso ya jaddada ƙudirin Gwamnati na haɗin gwiwa da abokan huldar ci gaba domin samun tallafin kuɗaɗen bunƙasa harkar noman daga takwarorinta.

Ya yi nuni da cewa Gwamnati mai ci a Jihar kamar yadda akayi tsammani, ta tunkari matsalar noma gaba daya don samar da ayyukan yi, da kawar da talauci da kuma tabbatar da samar da abinci a Jihar.

A cewarsa “Gwamnatin Jihar Neja ta kuduri aniyar kawo dabarun noma, kuma a shirye ta ke ta ci gaba da tallafawa ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai bunkasa tare da biyan manoman kuɗaɗe da tallafin IFAD.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet