Connect with us

Lafiya

NCDC Ta Fitar Da Rahotan Adadin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Kwalara A Bana

An samu rahoton mutuwar mutane 84 daga cutar kwalara, yayin da ake zargin mutane 2,860 sun kamu da cutar daga watan Janairu zuwa 27 ga watan Agustan 2023, kamar yadda bayanai daga Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Kasa ta bayyana.

Rahoton halin da ake ciki na makonni 31 zuwa 34, wanda aka fitar a ranar Laraba ya nuna cewa jihohi 25 a cikin kananan hukumomi 124 ne suka bayar da rahoton bullar cutar, inda adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai kashi 2.9 cikin dari.

Kwalara cuta ce mai saurin kamuwa da gudawa ta kwayoyin Vibrio cholerae. Mutane na iya yin rashin lafiya lokacin da suka ci abinci ko ruwan gurbatacce da kwayoyin cutar kwalara.

Kwayar cutar sau da yawa tana da sauƙi ko kuma ba ta da alamun cutar, amma wani lokaci yana iya zama mai tsanani kuma yana da haɗari ga rayuwa.

A Najeriya cutar kwalara cuta ce da ke yaduwa a lokuta da dama, wacce ke faruwa a duk shekara galibi a lokacin damina kuma galibi a wuraren da ba su da tsafta.

Rahoton halin da ake ciki na kwalara ya nuna cewa, daga cikin wadanda ake zargin tun farkon shekarar, kananan yaran da ba su wuce shekaru biyar ne suka fi kamuwa, sai kuma masu shekaru biyar zuwa 14 a jimillar maza da mata.

Haka kuma, rahotan ya nuna cewa daga cikin wadanda ake zargi, kashi 51 cikin dari maza ne, yayin da kashi 49 kuma mata ne.

Jihohin da suka kai rahoton bullar cutar a kasar ya zuwa yanzu sun hada da jihar Zamfara, Cross River, Katsina, Bayelsa, Ebonyi, Niger, Abia, Jigawa, Kano, Ondo, Borno, Kaduna, Bauchi, Sokoto, Plateau, Gombe.

Sauran jihohin sun hada da Oyo, Adamawa, Kebbi, Benue, Rivers, Ekiti, Imo, Osun, da kuma jihar Anambra.

“Zamfara (787) sun kai kashi 28 cikin 100 na duk wadanda ake zargi da kamuwa da cutar a cikin jihohi 25 da suka kamu da cutar kwalara. Karamar Hukumar Obubra (515) a Jihar Kuros Riba ce ke da kashi 18% na dukkan wadanda ake zargin sun kamu da cutar a kasar nan.

“A cikin jihohin da abin ya shafa, Cross River na da (718), Katsina kuma tana da (302), sai jihar Bayelsa mai mutane (265), Ebonyi tana da (227), sai Niger mai (136) da Abia take da (118) ke da kashi 62 na wadanda ake zargi a wannan shekara,” rahoton ya bayyana a wani bangare.

Kwatankwacin haka, ya ce wadanda ake zargin sun kamu da cutar kwalara a cikin shekarar da muke ciki sun ragu da kashi 63 cikin dari idan aka kwatanta da abin da aka bayyana a mako na 34 a shekarar 2022. Haka kuma, adadin mace-macen da aka samu ya ragu da kashi 67 cikin 100 a shekarar 2023.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet