Tsaro
Sojojin Nigeria Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Yiwa Rundunar Sojan Gona
Rundunar sojojin Najeriya runduna ta 9, dake Ikeja Cantonment, a jihar Legas, ta kama wasu mutane biyar da ake zargin sojojin Najeriya ne na bogi.
Wadanda ake zargin da aka mika wa ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu, an ce an kama su a lokuta daban-daban a yankunan Ojodu Berger, Ikorodu, Ogba, da Ikeja a jihar.
Wadanda ake zargin dai sun hada da Johnson Ayemoba, Salami Olamilekan, Mumammed Bilyaminu, Abijo Taofeek, da Adewale Quadri, a cewar daraktan hulda da jama’a na runduna ta 9, Manjo Augustine Kolawole, an kama su ne a wani sintiri na yau da kullun da rundunar ta yi.
Yayin da ake yi musu tambayoyi, Ayemoba ya yi ikirarin cewa wani abokinsa ne ya ba shi rigar.
Ya ce ina aiki ne a matsayin mai samar da tsaro a wuraren taro kamar Ikeja, Lekki, da Victoria Island. Na sami rigar daga abokina, Tiger. An kama Ni ne a Ikeja a lokacin da ba na sanye da kakin soji amma cikin kayan farar hula. Na dauki wannan hoton ne a lokacin zagayowar ranar haihuwata.
Dangane da Olamilekan, ya bayyana cewa ya sanya rigar ne domin raka motoci a ciki da wajen Legas, inda ya ce ya samu rigar ne daga wani mutum da ya bayyana sunansa da Tiger, wanda ake zargi na farko ya kuma gabatar da shi.
Yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan kamun, Major Kolawole, ya ce wadannan ƴan ta’adda sun kasance suna nuna kansu a matsayin sojojin Najeriya, suna tada tarzoma, suna yin sata ta hanyar yaudara, yayin amfani da kakin soji.
Wadannan ayyuka, sun zubar da mutuncin sojojin Nijeriya a tsakanin yan kasa masu bin doka da oda.
Wannan shedikwatar za ta ci gaba da kiyaye ka’idar aikin sojan Najeriya, da’a, kyawawan dabi’u, da kuma akidar sojoji, don haka, ba za ta taba lamunta da shigar da sojoji cikin duk wani aiki da zai cutar da ‘yan kasa masu bin doka da oda da ake son su kare lafiyar su ba.
