Connect with us

Tsaro

‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga a daren ranar Asabar sun kai hari gidan Tijjani Malumfashi da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina inda suka yi yunkurin yin garkuwa da mutane da dama.

‘Yan ta’addan sun kai kimanin 50, sun afkawa yankin ne da misalin karfe 11:00 na dare inda da isarsu suka fara harbin iska.

‘Yan ta’addan da suka raba kan su gida-gida, an ce sun fito ne daga wani gida zuwa wancan, inda suka fito da mutane kafin daga bisani ‘yan sanda da sojoji da ‘yan kungiyar ‘yan banga suka kawo dauki.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar The PUNCH a ranar Lahadin nan cewa, sakamakon zuwan jami’an ‘yan sanda da sojoji, wadanda aka yi garkuwa da su ciki har da wani alkali mai suna Alkali Sa’idu, an kubutar da su daga inda ‘yan ta’addan suka tara su.

An tattaro cewa, an fito da mutane a kalla shida daga gidajensu, an daure su, an rufe musu fuska kafin isowar jami’an tsaro.

“Jami’an ofishin ‘yan sanda na yankin, a Malumfashi, tare da tawagar ‘yan sanda, da sojoji, da kuma ‘yan banga, sun yi nasarar dakile harin,” in ji majiyar.

Ya kara da cewa, “An yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ‘yan ta’addan da jami’an tsaro sama da sa’a guda kafin su (’yan bindigar) su tsere.

“Amma daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, fitaccen dan kasuwa, Alhaji Zaharaddeen, wanda aka fi sani da Danmaliki, ‘yan bindigar sun harbe shi kuma a halin yanzu yana jinya a babban asibitin Kwandala, da ke Malumfashi,” inji majiyar.

A halin da ake ciki, mazauna garin Malumfashi na ci gaba da jinjina wa Baturen ‘yan sandan yankin DPO, Bello Umar, da sojoji bisa yadda suka shiga tsakani a kan lokaci tare da nuna bajintar akai, wanda ya hana barayin garkuwa da mutane da dama a yankin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar, ASP Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin kuma za ta tuntubi wakilinmu.

“Eh, muna sane da lamarin amma an fara bincike kuma za mu sanar da ku sakamakon da aka samu daga baya,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet