Labarai
Sojoji Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Da Hannu A Sace Daliban Jami’ar Jos
Jami’an runduna ta musamman ta soji a jihar Filato ta ce jami’anta sun kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane guda 89 a Filato da jihar Kaduna mai makwabtaka da jihar.
Jami’in yada labarai na rundunar, Captain Oya James ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Alhamis.
James ya ce rundunar ta gudanar da ayyuka daban-daban a cikin makon da ya gabata wanda ya haifar da sakamako mai kyau.
Ya kuma kara da cewa rundunar ta kama wasu mutane hudu da ake tuhuma a cikin wannan lokaci da aka kama tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su da kuma shanun da aka sace.
Ya ce, “Dakarun ‘Operation Safe Haven’ a Operation Hakorin Damisa IV, a wasu ayyuka da aka kaddamar daga ranar 25 ga watan Satumba zuwa 4 ga watan Oktoban 2023, sun kama mutane 91 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da daliban Jami’ar Jos, a harin kauyen Takania, da lalata gonaki, fashi da makami, safarar miyagun kwayoyi da satar shanu, da dai sauransu.
“Shahararrun masu garkuwa da mutane: Bashiru Musa da Idris Abdulrahman, wadanda ke cikin jerin sunayen ‘yan kungiyar OPSH da ake nema ruwa a jallo, an kama su ne a kauyen Mista Ali da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
“Wadanda ake zargin a lokacin da ake yi musu tambayoyi sun bayyana cewa suna da hannu wajen sace dalibai bakwai na Jami’ar Jos a watan Yulin 2023. Kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya dauke da alburusai 12 na musamman na 7.62mm.
“Rundunar sojojin da ke aiki da sahihan bayanai sun kama Mista Goma Abubakar da Jibril Abass kan harin da aka kai kauyen Takania da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar Kaduna, inda aka kashe mutane shida cikin jinni.”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Kwamandan ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu idan an kammala bincike.

Pingback: Hukumar Alhazai Ta Katsina Ta Kayyade Kashin Farko Na Kudin Hajjin 2024 - KAKAKI HAUSA