Connect with us

Labarai

Tawagar Jami’an Tsaro Sun Dakile Wani Yunkurin Zargin Yin Fashi A Banki

 

Wata tawagar jami’an tsaro ta dakile wani yunkurin yin fashi da makami a wani sabon bankin da ke unguwar Mushin a jihar Legas.

Jaridar Punch Metro ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 26 ga watan Satumbar 2023, da misalin karfe 10 na dare.

An bayyana cewa dan fashin ya tsallake babbar kofar shiga bankin inda ya samu shiga dakin ajiyar kudin banki ta silin.

Wata majiyar ‘yan sanda a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, wanda ake zargin da har yanzu ba a tantance ko wanene ba an kama shi sanye da abin rufe fuska lokacin da ya aikata wannan aika-aika.

Majiyar ta ce, “Wani wanda ba a san ko wanene ba sanye da abin rufe fuska ya shiga dakin bankin ta sili da misalin karfe 10 na dare. A lokacin da ya samu shiga, sai ya tafi kai tsaye sashin tsabar kudi na bankin.

“Daya daga cikin jami’an tsaron da ke aikin dare ne ya ji hayaniya a zauren bankin. Yana shiga ya binciki karar sai yaga wani a rufaffiyar fuska ya shiga sashin kudi na bankin. A lokacin da dan fashin ya gan shi, sai ya garzaya zuwa inda ya fito, ya tsere ta silin.”

Majiyar ‘yan sandan ta ce abokan aikinsa bayan an tuntube su, sun je bankin da misalin karfe 1 na dare, inda suka killace wurin tare da fara neman wanda ake zargin.

“Lokacin da ‘yan sanda suka isa bankin, sai suka binciki dakin banki da silin. Sun kuma binciki dakin janareta amma ba a gano wanda ake zargin ba. An dai ci gaba da bincike tun da safe amma ba a kai ga gano wanda ake zargin ba.

Ya kara da cewa, “A yayin da suke kara tsananta bincike, an ga sawun wanda ake zargin kuma an gano cewa ya tsere daga rufin gidan zuwa wani gini na gaba.”

Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa, ba a samu asara ko barna ba bayan da aka kirga kadarorin bankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

“Ya faru kuma ana ci gaba da bincike,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet