Addini
Hukumar Alhazai Ta Katsina Ta Kayyade Kashin Farko Na Kudin Hajjin 2024
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina ta sanya Naira miliyan 3 a matsayin kudin ajiya na farko ga kowane maniyyaci da ke son zuwa aikin hajjin 2024.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu-Kuki, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Katsina a wani taron manema labarai.
Ya kuma bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON, ta baiwa jihar kujeru 4,513.
KARANTA LABARIN Sojoji Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Daliban Jami’a
“Bisa la’akari da canjin kudi na Naira zuwa Dala, hukumar ta bukaci maniyyatan da ke da niyyar yin ajiya na farko na Naira miliyan 4.5.
“Mai girma Gwamna Dikko Radda ya amince da kudirin hukumar na raba kudaden a cikin wa’adin watanni uku da fara saka adashin gata na Naira miliyan uku, da kuma biyan su duk wata.
“Don haka, nan da Disamba 2023, maniyyata da masu ajiya za su kammala biyansu cikin kwanciyar hankali, kuma su jira duk wani adadin kudin aikin Hajji da Hukumar NAHCON ta bayyana,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa dole ne a biya dukkan kudaden ta hanyar daftarin banki da aka ba da izini ga hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina.
Babban daraktan ya kara da cewa dole ne a gudanar da rijistar a ofisoshin shiyya guda bakwai na hukumar da ke Katsina, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia, Daura, da Mani.
A kan shirye-shiryen farko Nuhu-Kuki ya bayyana cewa ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da takardar share fage na aikin Hajjin 2024.
“Takardu sun bayyana karara kan lokacin aiwatar da dukkan muhimman ayyuka tare da tsayar da ranar 20 ga watan Shawwal 1445H daidai da 29 ga Afrilun 2024, a matsayin wa’adin rufe tashar yanar gizo da kuma dakatar da bayar da bizar mahajjata da sauransu,” inji shi.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa, Nuhu-Kuki ya ce dole ne masu ajiya su kuma sanya hannu kan takardar amincewa da kujerar aikin Hajji a wurin rajista.
Don haka ya bukaci maniyyatan da su nemi ilimin aikin hajji daga wajen malamai domin samun damar gudanar da aikin hajji karbabbe. (NAN)
