Siyasa
Shugaban NNPP Na Kasa Na Farko Ya Musanta Samun Rabuwar Kai A Jam’iyyar
Wanda ya kafa Jam’iyyar NNPP kuma shugabanta na kasa na Farko Dr. Boniface Aniebonom ya mayar da martani ga masu cewa akwai rabuwar kai a jam’iyar musamman tsakaninsa da Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban Kasa a zantawarsa da manema labarai.
“Abinda zan ce shine dukkanin ‘ya’yan jam’iyar NNPP su kwantar da hankalinsu muna nan muna shirin daukaka kara game da wannan hukunci da kotun karararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke”.
“Babu wani rabuwae kai a cikin Jam’iyyar NNPP, Ka taba jin Dr. Kwankwaso ya ce wani abu akan abubuwan da suke faruwa a cikin social Media, ko ka taba jin Ni a matsayina na wanda ya kafa jamiyyar Na NNPP na ce wani abu”?
“To me yasa mutane za su dinga cewa akwai rabuwar kai a cikin jamiyyar? Wasu lokutan idan ka bar yara suka sake shine wasun su za su dinga neman sai sun yi tasiri. Wasun su suna neman gurin zama ne a cikin tsarin”.
“Wannan ba matsala ba ne, magana ce ta zabi kowa yana da damar yin zabin da ya yi masa. Amma hakan ba yana nufin akwai rabuwa kai a cikin jam’iyyar NNPP ba ne.
“Amma idan ka ji na ce wani abu ko Kwankwaso ya ce wani abu to shine sai ka fara bin ba’asi. Amma a yanzu dai babu wani rabuwar kawuna a cikin jam’iyyar NNPP”.
