Connect with us

Siyasa

Ganduje Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan Kano

 

Shugaban jam’iyyar APC, na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya magantu game da nasarar da jam’iyyar ta samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da aka gudanar a jihar Kano.

Jaridar Kakaki Hausa ta rawaito cewa kotun ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe, inda ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya tsaya takara a jam’iyyar NNPP.

Gwamna Ganduje wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar ya ce bai yi mamakin hukuncin ba domin ya riga ya san abin da ya faru a lokacin zaben.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Da yake magana da BBC Hausa a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, ya ce, “Yanda nake fatan kana nan da ka gani da kanka. Na yi matukar farin ciki da hukuncin. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Muna kuma gode wa bangaren shari’a da suka ba da damar yin adalci.

“Ban yi mamaki ba domin duk mun ga abin da ya faru a lokacin zaben. Na biyu, jama’a sun yi ta yi wa jam’iyyar mu addu’a don neman taimakon Allah don dawo mana da kujerarmu.”

Dangane da matakin da NNPP ta dauka na zuwa daukaka kara, Ganduje ya ce ita ce damar da dimokuradiyya samar.

“Wannan wani tanadi ne na doka, idan ba ku gamsu ba ku daukaka kara. Babu laifi a kan hakan. Tsarin kasar ya tanadi daukaka kara. Za mu hadu a can mutane suna yi mana addu’a.

“Ba mu da tsoro, mun yi imani da Allah, kuma duk wanda ya yi imani da Allah zai samu nasara da yardar Allah,” in ji shi.

Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya da ci gaba, inda ya ce tuni sun aza harsashin ayyukan ci gaba a jihar da za su sanya a gaba.

“Muna godiya ga mutanen jihar Kano nagari kuma muna ba su tabbacin cewa mun samu kokensu kuma za mu yi kokarin magance su. Muna gode musu saboda hakuri a wannan lokacin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet